Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M78
===DAGA BAKIN MAI ITA===

=== DODO KASHI NA BIYU===

Gabatarwa

A kashi na farko na hau sunan wani na yi rubutu akan Dodo,Wanda Dr Tahir na Jami,ar bayaro kano ya fada a hirarsa da rfi. Ku ma in mai karatu ya bi wannan shafin to lallai ya gansa. A cikin tsoka cin da anka yi na ga abin da ya ba ni mamaki da dariya. Ko da ya ke abin haka ya ke "KO CIKIN DUHU TALAKA YASAN DANAI." Wannan ko tantama babu ko,talaka ya gane dansa. Had ma Dan ya bayyanawa mahaifin da Duniya shi Dan talakan ne.

Bayanin dai na dakta an gansa. To yanzu sai muji na farfessa Aliyu Muhammad Bunza. Wanda shi ya yi littafen sukutum akan All,adar kuma ya cire Babu daya akan dodo. Sannan babin na iya daukar akalla daga shafi daya zuwa shafi goma sha biyar.

"Gabatarwa.....

Dodo wata halitta CE da hausawa sunka kakaba ko kirkira don cimma wata manufarsu. Musamman Saraki a lokacin jahiliya.

Bayan dogon Mazarin da na yi game da bayanin Bunza,na yi yan tambayoyi ga mutane mayawata. Musamman Direbobin Babbar mota,saboda sunfi kowa Shiga Daji da dare ko rana,sunfi kowa yawon garuruwa.

Wani yaya na Abu Dan kawu(Well-done) Wanda ya yi min bayanin dai dai da na Bunza. A cikin littafen Bunza ya Dan tsakuro bayani akan dodo das na kasar yarbawa. Shi kuma Abu Dan kawu ganau ne.

Ga yadda hirar mu ta kasance:

A.d. : A cikin yawonka kataba ganin Dodo?

Yaya well-done: Hakika ni da wani abokina mun sauka wani gari(Na manta grain da ya fada) anka ce kada kowa ya fito, a yau cikin dare. Saboda dodo za ya fito. Da munka ji haka sai munka ce yau ko muna shirin ganin Dodonnan da ake ta bayani. Sai munka samu wani dogon gida can sama munka haye. Mu na jiran ganin Dodo. Su kuma mutanen grain kowa ya shige gidansa. Mu na zaune ni da abokina a sama.sai munka ga wasu mutane cikin wata fita ta alamar tsafi, don kayan da suke saye da su da irin sabbatun da su ke. Tun anan na tabbatar da ba dodon gaskiya ba ne."ABU DAN KAWU SHI YA BAN WANNAN BAYANI, Kuma sanannen direba ne. Don shi kawon da ake cewa abokin su Ado Bado ne da Manu Tarankyal, yaran su rumfar mai gadi ne. Rumfar mai gadi kowa Baba Nana ta fannin uwa.

Farfessan Al,ada Bunza

Ya ce babu dodo ko tun asali donko ya fadi hujjoji akan hakan. Kamar haka:

Idan zan takaita.

Don Allah ko,a akwai Wanda ya ga Wanda ya zo guda ne ya ce dodo ya koro shi?Amsa babu.

Akwai mai gaya muna siffar jikin dodo kamar yadda zamu iya ba da siffar Aljani da mutum da dabbobin gida da na Daji?Amsa ba su kambala.

To bashin da masu Mazarin al,ada sunka bi Hausawa anan shi ne sauran Sassani jikin Dodo tunda munka iya yarda da:

1.Ba mutum ba ne,ba Aljani bane,Ba dabba bane. Saboda duk kan wadannan tsoronsa suke.

2. Kato ne maras tausayi ga Sauri kamar walkiya.

3. Ya na da kahoni

4. Ya na da kwadayi

5. Ya na da kafa BIYU

6. Ya na da hakora zago-zago

7. Yana da girma.

A haka a ke bayaninsa

To ga bashin da masu Nazarin al,ada sunka biyo hausawa:

1. Yaya Wuyan dodo ya ke?

2. Yaya cikinsa yake?

3. Yaya hannuwansa su ke?

4. Yaya takon kafarsa suke?

5.wacce irin halitta ce,don shi Ba Aljani ba ne,Ba mutum ba,Ba dabbobin da munka sani ba.Ba mala,ika ba.To mene ne shi?

KARIN BAYANI

Kamar yadda anka fada baya,bincike ya nuna Sarakin jahiliya su na amfani da Kalmar Dodo ne Kawai don tsoratar da jama,a. in ba a son mutum ko ya yi wani babban laifi sai a ce rana kaza za aba Dodo shi.To alokacin jahiliya kowa yasan akwai cinikin Bayi tsakanin Sarakuna da Turawa da larabawa. To kuma har wa yau in kana kallon fina-finnan su.Ko Allah ya kai ka kana ganin bakar fata a cikin su. To wannan yana da taliki gida uku. Koma fiye,amma na dodo ya fi karfi. Saboda sayar da bakar fata da a ke yi ga larabawa da turawa ne. A matsayin Anba dodo. Kuma mutane ba su zuwa su ga yadda ake ba Dodo naman Dan uwansu ko Dan uwansu. Saboda kada a hada da su.

A takaice dai ni ban samu takamaimen bayanin da ya gamsar da ni ba akan Dodo.Ban hana zuwa gaba ba .ko shi sai an samo min ansar tambayoyi na. Sannan in yarda. Na bi sahun Shaihina na ala,ada Bunza. Ina jira har ko yaushe ne.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124