Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M81
Al,ada:===KETARE HABA===

BUNZA,A.M.(2006) "Duk abin da bahaushe ya fada na kariyar lafiyarsa da kariyar tarbiyarsa to sai da ya yi ta gwadawa. Kamar Karen magana ds."

Wata all,ada ce na tuna da it's wadda iyaye mata kewa yayansu.Ni ma dai na Shiga a cikinta, Shi yasa ban mantawa.Alokacin muna yara idan zamu tafi makaranta akance sai mun KETARE HABARMU. Sai mun Dan sha wani Abu,kada maye ya kama mu. Ko kumallo.dasauransu.

Galibin mutanen dori Kasan muradinsu dai dansu ya yi karfin jiki da na aiki da juriyàr wahala. Saboda aiki da ko ta kwana.

Shi Bahaushe har ko yau she a kimiyance ya ke lamarinsa,kuma wannan kimiya da ilmi ya na bin koyawar addini sau tari.

To abin da na hango ga KETARE HABA ganin na ke wayo ne na Bahaushe na rashin cin ko mai na iya haifar da matsala, mu samman ga yaro. Don haka sai a yi farau-farau ko aba shi Hura ko kunu. Kafin ya fita,koda ya je Lamarin kurciya,ko wani aiki ya dauke masa hankali baya jin wata damuwar da zata kawo mai màtsala kai tsaye. Wannan bai tsaya kan kananan yara Kadai ba. Hatta many an mutane da anka koya ma Galibi ko ruwa ne sai suñ sha. In ba da wata lalura mai karfin ba.

Abin mamaki Bazabarme ya fi Bahaushe na ciya a kan wannan. Shi Bazabarme in dai game da abinci ne fa to bawasa. Jiya wani Bazabarme ke kari tun karfe Bakwai da mintuna goma. Kuma ya na sauri wai ya yi (letter) ya makara.wannan dibara abin koyi ce. Saboda Barin yaro ya fita gida bai ci ko mai ba a gaskiya ba dai-dai ba ne.mu assalam.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124