Tsame Rubutowa
abubakar m. damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M9


TUKE:TARNAKI:TUKUKI :TUKUDI DA SAURANSU:

1.TUKE: Shi ne abin da Dabbobi har ma da dan Adam. Ke yi a wani Karon bayan sun ci Abinci. 2.TARNAKI: Shi kuma jaki ake wa shi,ba Dabaibiya ba. Dn Dabaibiya kafafun gaba a ke yi wa.TARNAKI: Kuwa kafar baya da ta gaba ake daurewa. Ku ma ana wa Mutum,shi kuma nasa daban ya ke.3.TUKUKI: Tashin Abu sama kamar I ska ko Hayaki. A kwai kuma itaciya ko haki ya na magani sosai. Musamman ga yan Tauri . Ya na korar jini,ya na sa saurin fushi,ya na maganin kaifi.Ga yada shahararen dan taurinnan na kasar HAUSA da Alh. GARBA DAN WASA ya tada (zuga) shi."....Ka hwada ma Rabin Yabo da Kura Matar Shehu daka dai su Kama hanyar dama. Ni ko in Kama hanyar hauni. Dn na ci Tauri,na ci Tamako, na hada da Gazal Giwa,na hada da sayen TUKUKi,baba na sha Madacci ya halaka ni......"Balan Barga.

TUKUDI

Ba hura ba ne,ba gumba ba ne. Ra,ayin mutane: malam umar Junji,Shehu Gusau,Muhamda Maradi,Malam Aminu Jegga,Mudassir Zariya,Umar kaura( abokina)sunce"Gero ne za a dake, sai ya yi gari, ba a fitar da kasari, ballai tsagaro. Ba a fitar da Dussa da sauransu. Haka da sunka daka sa,haka kawai ake saka masa Nono a sha. Malam Umar junji, ya tabbatar min da sun yi shansa,in za su je Gona tun da safe. Watau in babu hura ko wani abinci.Sai a yi TUKUDI dn a yi sauri a sha a tafi Daji.Shi kuma Kaura da Aminu sun Kara da cewa" Ya na Kara jini musamman ga matan da ke jigo (Shayarwa)DS.

Kayan cikin TUKUDI

1Gero ko maiwa in ya zama dole watau babu Gero.

2. Nono.

3. sauran magungunnan gargajiya ga Mai shayarwa.

Dkkan kalmomin da munka yi bayani saiwar kalmarsu "Tu" Ku ma kusan dukkansu su na da kamar ma,ana daya.

Idan na yi kure a gyara min don Allah. Dn kunfi kowa sanin karamin Dali I ne ni. Musamman a cikinku.ABUBAKAR M. DAMMA( A.D.GORA)

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124