Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M93
===Wani boyyen ilmi a karamin yaro===

Yaro na kowa. A jiya na kara wata fahimta ga karamin yaro. Ga bin da na gano a Kansu:

1. Idan karamin yaro na a hannun wani ko mahaifiyarsa. Ka Tara hannu alamar ya zo ya na kin zowa. To ka yi kakarin da za ka yi dibarar da zai zo ko ba a wannan sa,a ba. In ka dauke shi, ka Dora goshinka da na sa,ka Dan girgiza kanka yadda bai damuwa ko dimauta. Za ka ga ya yi dariya, ko kuma in kuka ya ke zai yi shuru.

2. Idan kana son Jan hankalinsa ga ya dutda abin da ke bakinsa. Sai ka ce too! Ka Nuna bakinka gefen hagu. Za ya tudda abin da ya sa a bakinsa.

3. Idan kana son ka nuna mai abinnan akwai dadi. Sai ka bugi kanka sau uku. Za ka ga shi ma ya buga, In ya iya. In bai iya ba kuma za ka ga ya yi dariya. Ma,ana ya ji dadi kenan.

4.Idan kana son da ka shigo gida,ya rugo ga reka. Karinka sawo mai yan kayan zaki. Amma an an sai ka yi hankali,saboda wasu daga cikin kayan dadin Suna cutarwa gare su.

5. Idan ya sheko a guje,kai ma yi Dan gudu koda na tako BIYU ne,ka tarbe shi. Ka dauke shi. Ka yi mai tawai. Za ya yi Dariya.

6. Idan za ka Barin gida, to ka ji fa aiki. Sai ka aike shi,ka fece abinka. Zai manta. Wani fa.

6. Idan kana son ya ji tsoro,sai ka yi irin kukan kyanwa. Zai ji tsoro.

7.Idan kana son ya shaku da kai sosai,ka rinka daukarsa,ka na wasa da shi. Kamar ka daukai. Ka aza shi a cikinka,kana kallonsa,kana fara,a.

8.Ka saba mai da baba ko mama ga Babba.

Ka saba masa da Baba ho,ga kowa ko mama ho. In ya iya magana.

9. In za ka fita gida ka rinka yi masa baye-baye,ka na nuna alamar da hannunka na dama.

10. Ku rinka cin abinci da shi,in ya iya.

11. Ka saba mai da sallama,in za ya Shiga wuri.

Yaro na son wadannan abubuwa sosai. Kuma suna da kyau. Za ka ga ya tashi da tarbiya mai kyau. Kowa na sonsa.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124