Tsame Rubutowa
Abubakar M. Damma(a.d.gora)
shkr 1 | 1009M94
====HASADA A NAZARCE KASHI NA 1===

Mun San duk Dan Adam baya da makiyin da ya wuce shaidan. Shi kuma shaidan ya dauko ta ne tun kafin halittar Annabin Allah Adam. Kamar yadda Ayoyi da kissoshi sunka baiyana. Ya yi alkawarin kai duk zuriyar Annabi Adamu (A.S) a wuta. Zai dai bayin Allah salihai.

To in na takaita yana bibiyar yan Adam ya na sake musu abubuwan da yasan Allah mahalicci bai so. Kamar ta farko cin itaciyar zakun. Dalilin da Allah ya Sauke Annabi Adam a kasa da shi Shaidan din. Na BIYU Hasada tsakanin habila da kabila.duk shairin shaidan ne.

Da ga cikin a kwai Hasadar da ya juya daga mutm zuwa mutum, ko daga ma,aikata zuwa ma,aikata, ko daga gungun mutane zuwa wani gungunsu.

==== MATSALAR HASSADA===

Bahaushe ya ce"HASSADA GA MAI RABO TAKI CE" Wannan tabbas gaskiya ne ,don babu Inda kaga mai HASSADA ya ci gaba. Misali shi Shedan da ya kago ta wane sakamako ya samu? TSINUWA DAGA ALLAH.Haka Wanda ya fara kisa. To ita HASSADA tana cin imani da mai da mutum baya akan ko mai nasa.

Kasani fa dun kawa mutum HASSADA Baka isa ka hana shi samun abin da ya ke rabonsa ne ba. Haka bai isa ya hana ka na ka Rabon ba. To mene ne za ya sa ka yi masa HASSADA? Harka yi kokarin yin wani Abu maras kyau akansa. Wanda in an yi ma ba za ka ji dadi ba? ZA MU CI GABA. IN ALLAH YA SO.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124