Tsame Rubutowa
Sharfaddeen Sidi Umar
shkr 1 | 1010M1
Maraba Lale Da Dawowar Makarantar Hausa

Cike da murna da farin ciki maras misaltuwa nake murnar sake dawowar Makarantar Hausa a bakin aiki bayan dogon hutun da ta tafi. Shakka babu babban Editan MH ya cancanci yabo da jinjina kan jajircewa, sadaukar da kai da aiki tukuru domin bayar da gagarumar gudunmuwa ga ci-gaba da bunkasa Harshen Hausa ta hanyar assasa MH da sauran dimbin aikace-aikace masu muhimmanci, alfanu da tasiri da ya shekara ya shekaro yana yi.

Muna sane da dimbin kalubale da tarnakin da MH ta ci karo da su da fadi tashin da Edita, Malam Bello Muhammad Danyaya ya yi ta yi a tsayin shekaru domin ganin ya shawo bakin zaren warware wadannan matsaloli ta hanyar dawowa da sabuwar ingantacciyar MH da karfin ta. Amma duk da haka Malam bai karaya ba, bai kuma yi kasa a guiwa ba wajen cikar burinsa na yi wa al'ummarsa babbar hidimar da ta zarta tunanin mai tunani. Alhamdulillahi a yau haka ta cimma ruwa.

Don haka muna matukar godiya tare da fatar alheri da rokon Allah ya kara daukaka MH ya kuma kareta da kariyarsa ya sa ta zama fitacciyar makarantar da Hausa da Hausawa za su rika alfahari da bugun gaba wajen bunkasa Harshe, Adabi da Al'ada.

Da fatar za mu bayar da dukkanin goyon bayan da ya kamata ga ci-gaba da dorewar wannan hamshakiyar Makarantar wadda ita ce irinta ta farko a Duniyar Malam Bahaushe.

Malam mun gode. Daliban MH sun gode.

Sharfaddeen Sidi Umar.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124