Tsame Rubutowa
Sharfaddeen Sidi Umar
shkr 2 | 1010M2
Rudanin Tunani: Yadda Makarantar Hausa Ta Daidaita Sahun Adabin Malam Bahaushe Da Al'adunsa

Daga, A'isha Ahmad

Sunan Littafi: Rudanin Tunani

Mawallafi: Bello Muhammad Danyaya

Shafuka: 99

Bugawa: Makarantar Hausa

Daukar Nauyi: Laftanar U.A Sidi

Farashi: 500

Shekarar Wallafa: 2012

Shekaru aru-aru da suka gabata, tun daga lokacin da Malam Bahaushe ya fara rubutawa tare da wallafa tunaninsa, an samu bullar mabanbantan littaffai daga alkaluman marubuta daban-daban, wadanda suka bayar da ta su gudunmuwa wajen fadakarwa, ilmantarwa da kuma nishadantar da al'umma daga kaifin hikima, basira, fasaha da zalakarsu.

Daga ciki, wasu marubutan da dama sun yi iyakar kokarinsu wajen ciyar da adabinsu a gaba, wadanda suke raye da wadanda suka karbi kiran mahaliccinsu, har zuwa kan bayyanar marubuta Adabin Kasuwar Kano, wadanda kalilan ne daga ciki za a iya cewa sun kokarta, galibinsu kuwa ai a bayyane yake cewar gurbata Adabin suka yi, daga ciki kuwa har da marubutan da 'yan uwansu marubuta ke da tabbacin littaffan da suka fitar Adabin Yarbawa ne suka wallafa a cikin taskar Adabin Hausa, wato irin abin nan da a ke kira ungulu da kan zabo.

A kan wannan an jima a na tabka muhawara tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin nazarin Hausa kan yadda ya kamata alkiblar rubuce-rubucen ta kasance; yayin da wasu ke ganin tsarin da a ke a kai, gurbataccen tsari ne, wasu kuwa na ganin a hankali yau da gobe jariri kan zama ango, wasu marubutan kuwa kunfar baki suke yi a kan abin da suka rubuta ba ya da masoka. A haka mafi rinjaye sun aminta da cewar akwai kwarkwata a cikin kitson wallafe-wallafen da a ka kitsa, daga tarikitan litaffai ire-irensu Idan Dera Da Sata..., da Kowa Ya Raina Tsaiwar Wata... da Da ko Jika? da litaffan baya-bayan nan kamar Aljani Ya Taka Wuta da kaddara Ko Kishi da Birni da kauye, da Gudun Talauci da Almajiri da sauransu da dama.

Farfesa Ibrahim Malumfashi wanda shine jagoran da ke kan gaba wajen fafutukar ganin an canza fasali da tsarin rubutun da a ke a kai, hasalima wanda shine ya kakaba masa sunan Adabin Kasuwar Kano, ya sha nanata cewar muddin a na son ci gaba da bunkasar Adabin Malam Bahaushe, to ya zama wajibi a sauya taku da salon tafiyar da a ke a kai, wadda babu abinda ta haifar illa jagorantar suka da caccakar duk wani littafin da ya fada cikin kundin Adabin Kasuwar Kano.

Ra'ayin Shehin Malamin na Adabi shine, sauya salon rubutun abu ne mai sauki, musamman ganin cewar akwai kwararrun marubuta wadanda ke da kwarewa da gogewa a fannin, wadanda idan suka haskaka fitilarsu, to ba shakka za ta yaye duhu.

A bisa ga wannan a bayyane yake cewar fitacciyar marubuciya Rahma A. Majid ita ce marubuciyar farko da ta fara karba kiran Farfesan na Adabi, ta hanyar wallafa mashahurin littafin Mace Mutum mai shafuka 520, daga madaba'ar Freedom Press Kaduna, wanda Malaman Adabi da dama suka yabawa hobbasar kwazonta kan aikin da suka kira Gagara Gasar Masu Gasa.

Abin lura a nan shine, baya ga Rahma, ba a samu wasu marubutan da suka nuna da gaske suke yi wajen karba kiran Malamin wajen Daidaita Sahun marubuta ba, domin babu wani littafi daga cikin daruruwan littaffan da suka fito wanda ya tsallake fadawa jujin Adabin Kasuwar Kano, baya ga littafin na Amina da Fatima Godiya.

A haka, wane tudu, wane gangare, bayan sanyawa al'amurran masana'antar adabi idanu na tsayin lokaci, bayan ganin shekaran jiya da jiya da yau ta lalace har tana kokarin shayar da gobe, Makarantar Hausa ba ta yi kasa a guiwa ba, wajen sharewa masu karatu hawaye ta hanyar bin ingantaccen tsarin da masana ke kururuwar a bi, domin bunkasar Adabin Malam Bahaushe da al'adunsa ta hanyar fitar da sabon littafin Rudanin Tunani daga taskarta.

Hakan ya biyo bayan fahimtar da Makarantar Hausa ta yi na dalilin sabanin da a ke samu daya ne, wato kasancewar Bahaushen yau, yana rayuwa ne a kan Adabi uku: Adabin Gargajiya, adabin Larabawa, da adabin Turawa.

"Dan shekara tis'in, adabin gargajiya ya yi masa yawa. Dan shekara sittin, adabin Larabawa ya yi masa yawa, kamar yadda kuma dan shekara talatin, adabin turawa ya yi masa yawa." Ganin cewar adabin kowane daga cikin wadannan ya yi ma kowane bangare yawa. A kan wannan Makarantar Hausa ta aminta da cewar "Idan a na son cimma matsaya a cikin Hausawa, to rubutun da a ke yi, ya kasance gamin gambiza, ya kunshi abin da kowane bangare ya sani. Haka kuma a cire abinda wani bangare ke kukan an kara, sa'annan a kara abin da wani bangare ke kukan an rage." A cewar Makarantar Hausa.

Marubucin littafin, Bello Danyaya ya tsara, ya gina ya kuma tayar da labarin ta hanya mafi kayaratwa da burgewa a cikin salo da sigar da marubuta da dama za su so a ce sune suka rubuta littafin, wanda a iya sanina shine irinsa na farko a wannan sigar.

Labarin wanda a ka saka a cikin Rudanin Tunani, daga shafi na 1 zuwa na 99, duk wani gini da a ka aza a ciki na fadakarwa ne. A ciki za a ga yadda Malami ke taka tsantsan wajen koyar da dalibansa a makaranta, domin gujewa aikata abinda ba dai-dai ba, akasin wasu marubutan wadanda ke rubuta cewar "Kyakkyawar kira da zubin halittar da ke gareta, mai firgita laccara ce a yayin gabatar da darasi."

Haka kuma marubucin ya nuna hikima wajen hada labarin Rashid da Rashida da kuma amaryarsa Nafisa, da kuma alakanta labarin mutuwar Nafisa da Gwamna Nomau Sallau.

Littafin duk da cewar ba na soyayya ba ne, samari da 'yan mata 'yan bana bakwai za su ga yadda ya kamata hirar Bahaushe da Bahaushiya ta kasance, akasin hirar shan minti da ke cikin galibin litaffan Hausa. Haka kuma shafukan littafin sun nuna yadda a ke kishi ba da hauka ba, idan ma an yi na haukar to ga wawakeken ramen da a ke fadawa.

Mutuwar Nafisa a safiyar da za a daura aurenta da hayagagar da ta biyo baya bisa zargin Kawu Audu ne ya kasheta ko kuwa Gwaggo Ladi ce, da halin kaka-ni-kayi da Rashid da mai dogon Gemu suka shiga, har zuwa yadda likita da jama'ar gari suka shiga rudu, duk ya nuna muhimmanci da fa'idar "Komai ka ji ka sake tambayawa, don ba mamaki ba ka ji dai-dai ba, ko wanda ya gaya maka, bai gaya maka dai-dai ba." A daya gefen kuma littafin ya karantar da mu "Kada mu yi aiki da tunanin wani, don yana yiyuwa ya yi kuskure a tunaninsa."

Shakka babu sunan littafin Rudanin Tunani ya dace da shi. Haka ma salo da sarrafa harshen da a ka gina labarin da shi ya kayatar, kamar yadda kuma a ka baiwa kowane bangare na adabin Hausa hakkinsa. Ko ba a fada ba littafin ya zo dai-dai a lokacin da a ke bukatarsa. Musamman yadda ya kaucewa shiga cikin kwamacalar littaffan Adabin Kasuwar Kano.

Sai dai a fahimtata, a inda marubucin ya kashe Amarya Nafisa bai yi mata adalci ba. Haka ma ya kamata a bayyana makomar zamantakewar Rashid da Rashida. Baya ga wannan mun ga tafiyar Gwamna Nomau da iyalinsa a kasar waje amma ba mu ga dawowarsa ba, ba a kuma bayyana inda suka tafi ba.

Wasu kura-kuran da na ci karo da su, sune:

Motaci maimakon motoci a shafi na 54.

Zanga-zangan nan maimakon zanga-zangar nan a shafi na 56.

Ta kara da ce wa maimakon ta kara da cewa a shafi na 66.

Kofin ku tafi maimakon kafin ku tafi a shafi na 90.

Daga karshe kamar yadda mai mukaddima, Dakta Hamza A.Ainu ya bayyana a cikin littafin, lallai ya kamata a sanya littafin nan a cikin manhajar karatun daliban babbar sakandare. Kamar kuma yadda zai taimaki daliban jami'a da duk masu sha'awar nazarin adabin Hausa.

An wallafa a LEADERSHIP Hausa ta ranar 15 ga Fabrairu 2015 shafi na 29.

Ahmad ta rubuto ne daga, unguwar Hotoro, Kano.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124