Tsame Rubutowa
Sharfaddeen Sidi Umar
shkr 1 | 1010M3
Yadda Taron Bunkasa Adabi Ya Kayatar A Sakkwato

"Sidi Ya Daga Darajar Sakkwato" Cewar Dakta Mansur Isah Buhari

..."Dalilin Da Yasa Nake Wallafa Ayyukan Adabi" -In Ji Babban Soji, Kwamanda Sidi Dogon-Daji

A kokarin bunkasa sha'anin ayyukan Adabi da dabi'ar karatu a cikin al'umma, kungiyar Caliphate arts and Literary Forum ta shirya kasaitaccen taron habaka rubutu da inganta shi ta hanyar shirya taron musamman na karatun fitaccen littafin rubutaccen wake mai suna 'Poet of Dust' wanda hadakar littafin rubutattun wakokin Turanci ne wanda kamfanin Konya Shamsrumi da Parresia Press suka wallafa dauke da shafuka 80.

Mawallafin littafin Umar Abubakar Sidi (Abubakar Sidi Umar Dogon-Daji) babban jami'in soja ne a Rundunar Ruwa ta Nijeriya wanda ke rike da mukamin Kwamanda haka ma matukin jirgin saman sojan ruwa ne mai saukar ungulu. Marubuci ne da ya rubuta littaffan rubutattun wakoki, labaran hikiya da gajerun labarai daga ciki akwai Striking The Strings da kuma The Sword of Barbushe (Takobin Barbushe)

A yayin da yake bayyana makasudin shirya taron, Shugaban Kungiyar Caliphate Arts and Literary Forum, Khalifa Aliyu Adamu ya bayyana cewar babban aikin da suka sa a gaba shine kokarin bunkasa ayyukan Adabi domin samun ci-gaba mai amfani a cikin al'umma. Ya ce littafin Poet of Dust na Umar Sidi yana daga cikin ayyukan Adabi da suke da kima da tasiri wanda suka ga dacewar shirya taron musamman domin karatun littafin tare da bitarsa.

"Ya ce wannan ba karamin ci-gaba ba ne. Mu kan tara matasa masu hazaka, marubuta da mawaka mu tattauna ayyukan su a kowace ranar Lahadi tare da musayar ra'ayi kan baiwar da Allah ya yi masu. Littafin Sidi, littafi ne da aka yi baje-kolin hikiya da fasaha wanda tabbas abin alfahari ne a Duniyar Adabi kuma kamar yadda kuke gani taron ya kayatar matuka." Ya bayyana.

A taron wanda aka gudanar a American Space da ke cikin makarantar share fagen shiga jam'ia a yau Lahadi, mawallafin littafin Poet of Dust, Umar Abubakar Sidi ya bayyana cewar ya rubuta littafin ne domin adana tunanin sa da hangensa kan al'amurra daban-daban.

Ya ce "Rubutattun wakoki gadon Sakkwatawa ne mai dimbin dadadden tarihi. Magabatan mu kamar Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo, da diyarsa Nana Asma'u da kanensa Abdullahin Gwandu duka sun yi mabambantan rubutu kan rubutattun wakoki masu ilmantarwa da fadakarwa wadanda har yau a na karatun su. Zan yi kokarin fassara littaffai na domin amfanin al'ummar mu kamar yadda jama'a suka yi kira."

A taron Farfesa Asabe Kabir Usman, Dakta Tahir Malam da Dakta Mansur Isa Buhari na jami'ar Usmanu Danfodiyo duka sun tofa albarkacin bakin su kan rubutattun wakoki, tasirinsu da muhimmancin su a Duniyar Adabi. Haka ma an gabatar da tambayoyi daya bayan daya daga mahalarta taron kan littafin da abin da ya kunsa wadanda duka mawallafin ya amsa dalla-dalla.

Dakta Mansur Isa Buhari ya bayyana cewar duniya bakidaya ta san da zaman rubutattun wakoki. Ya ce a duk lokacin da aka samu rubutattun wakoki za a samu farin ciki, idan aka samu farin ciki za a samu zaman lafiya, hadin kai da fahimtar juna idan kuma aka samu zaman lafiya za a samu ci-gaba. A kan wannan ya ce yana da kyau jama'a su fahimci rubutattun wakoki da muhimmancin su a cikin al'umma. "Mutanen mu ba su cika mayar da hankali kan rubutacciyar waka ba, aikin da Sidi ya yi ya daga darajarsa ya kuma nuna irin hazikan mutane ma'ilmata da muke da su a Sakkwato wadanda duk duniya suna iya shirya abin da za a yi alfahari da shi." Ya bayyana.

Fatima Isa Wasagu daga Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari ta bayyanawa manema labarai cewar "Muna alhahari da Sidi da ayyukansa na Adabi domin ya rubuta littafin da ko a qasar waje zai iya shiga gasa da Turawa kuma ya yi nasara a kai.

A zantarwarsa da manema labarai, fitaccen marubuci kuma Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Tambuwal, Malam Yusuf Dingyadi ya bayyana muhimmancin da ke akwai ga mawallafin da ya fassara rubutunsa da Hausa domin amfanin al'ummar Hausa da Hausawa domin yin hakan zai taimaka sosai wajen ilmantar da al'umma. Ya ce Gwamnatin Jiha ta na kokari kwarai wajen samun nasarar shirin ta na yaro daya littafi daya wanda hakan abin yabawa ne.

Baya ga Malamai a Jami'ar Danfodiyo, Jami'ar Jihar Sakkwato da Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari haka ma taron ya samu halartar gogagge kuma kwararren marubuci Sadik Abba Abubakar Jnr wanda yana daya daga cikin hazikan marubuta rubutaccen wake da Abdulrahman Jidda babban jami'i a Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) da dimbin masu ruwa da tsaki a ayyukan Adabi da dalibai maza da mata da marubuta masu tasowa wadanda suka bayyana littafin a matsayin daya daga cikin littaffan da aka bata lokaci da tunani wajen hada zaruruwansu cikin kwarewa da gogewa da lakantar ciki da wajen rubutu domin isar da sako da abin da ya sosa wa marubucin rai a littafin na Rubutaccen Wake kan Hasashe.

Muryar Kebbe/Tambuwal 8th Assembly.

29/12/2019.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124