Tsame Rubutowa
Aliyu bin aliyu
shkr 1 | 1019M6


Ya ilahal-Arshi gamu,

Yara Har Tsoffin cikimmu,

Duk Takaici ya Ishe Mu,

Ga ana faman kashe Mu,

Ba'a girmama tamu Rayuwa ba.

😭😭😭

.

Yau Arewa Maza da Mata,

Kuntatarmu tana yawaita,

Ga Musifu sun tsawaita,

Ga Shi kowa ya Kawaita,

Ba mu San Manufar Ubangiji ba!

😭😭😭

.

Mun zamo Guiwa a sare,

Kowanemmu Ido a zare,

Ko ana so ne mu k'are?

Namu Tarihi a share,

Tamkar ba'a yi mu Yan Adam ba!

😭😭😭

.

Rabbi ga Kukammu mun Kai,

Tunda ba me jimmu sai Kai,

Me isar Daukar matakai,

Zul-jalali ka ba mu jin-kai,

Kai ne Gatammu ba Mutum ba!

😭😭😭


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124