Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M13
Masu cin beraye sun bayyana a Kano.

A yayin da masana lafiya ke gargadin mu’amala da Beraye domin gujewa kamuwa da cutar Lassa sakamakon cutar an gano cewa Beraye ne ke hadda sa cutar ga bil Adama.

Sai gas hi wasu mutane da suka mayar da Beraye naman cimakar su a cikin abincin sun a yau da kulum.

Mutanen wanda suka ya da zango a cikin garin Rogo dake karamar hukumar sun ce cikin Berayen da suke ci babu wanda ya taba samun wata matsala ga lafiyar su, duk da cewa cutar Lassa ta samo asali ne ga Beraye.

Michel Joseph da shi da iyalai da ‘yan uwansa wanda suka sami masauki a cikin garin Rogo ya ce” Mu masu kama Beraye ne kuma ba mu san irin Berayen ba kuma bamu samu matsala da sub a, domin kuwa abincin mu ne Bera muna kama su kuma muna cin su, duk cikin mu babu wani wanda ya samu wata cuta gamunan garau muna zaune daram har kwado muna ci.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124