Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M14
An dauko ne daga shafin Bala Anas Babinlata.

SAKAMAKON ZAMANMU NA RANAR ASABAR 23/11/2019

Ya 'yan uwa marubuta, da masoya Hausa Novels Salamu Alaikum wa Rahmatul Lahi Wa Barakatuhu.

Mun zauna ranar Asabar kamar yadda aka tsara, haka nan mun tattauna abubuwa da dama da suka shafi littattafan marubuta na baya da na yanzu, da yadda makaranta zasu iya samun su idan suna bukata.

1. Da farko dai a taron an yarda akwai bukatar yin babban platform da zai kunshi kusan duk aiyukan marubuta. Amma an sanya shi a matsayin aikin da za a yi a mataki na gaba. Amma bukatar littattafan ta sanya muka tsayar da matsaya a kan za a yi amfani da website din okadabooks a matakin farko don fara kasuwancin a halin yanzu, ga bayanin nan a kasa.

Hanyar farko da aka fitar ta samun littattafan ita ce samar da Soft copy, wato littafin da za a karanta a waya, wannan ita ce hanya mafi sauki, sauri da arha tun da bata bukatar dab'i, bata bukatar delivery, wato ba sai an buga sannan a aikawa wanda ya saya ba, za a iya bude littafin a waya idan an biya, a karanta. Za a biya kudin littafin ta internet a okadabooks. Zamu yi cikakken bayani ga wadanda basu taba sayayya a website din okadabooks ba.

Hanya ta biyu ita ce yadda za a sayi bugaggun littattafai dake kan takarda. Ita wannan hanyar tana da harshen damo.

(a) Akwai littattafan da tuni ana da su a kasa, ma'ana masu littattafan sun buga su, kamar Idan So Cuta ne...... Na Yusuf Adamu, da In da So Da Kauna na Ado Ahmad Gidan Dabino da makamantansu.

(b) Haka nan akwai littattafan da sai makaranta sun bukace su sannan za a nemo littafin daga marubucin a biya a buga wa mabukata.

A nan (a) yana da sauki, tun da akwai kayan a kasa, aikawa kadai zai rage a yi idan mutum ya biya kudin littafin. Amma (b) sai wani adadi na masu bukatar littafin sun samu sannan za a iya bugawa, haka nan bugun zai yi tsada saboda 'yan kadan kawai za a biya Printer ya buga. Hanyar da makaranta zasu biya kudin wadannan littattafai kafin a aika musu zata zama ta bank Account da za a tanada.

Muna sa ran samun wata hanya da zata saukaka book on demand din, amma dai zamu jira har maganar ta nuna tukuna.

Haka nan akwai littattafan da sun yi nisa, ma'ana an taba buga su a baya amma yanzu sun bata, babu su babu elctronic copy dinsu, su irin wadannan littattafan ba zamu iya alkartawa masu bukatar su ba har sai idan makarantan dake bukatarsu suna da yawa, domin akwai dawainiyar lalubo littattafan da buga su a computer.

A game da matsalar marubuta da makaranta da ba sa iya sarrafa wayoyinsu yadda ya kamata, an ware mutum biyu da zasu taimaka da samar da tutorial a fannoni dabam dabam. Za a yi karin bayani a akan wannan, bayan mun ji shawarwarin ku na yadda za a tsara abin don ya zo da sauki.

Sannan an yi tsokaci game da karancin nagartar labaran da marubuta musamman sabbin marubuta ke fuskanta, aka kuma yanke Shawarar a samar da hanyoyin bita don karawa juna sani, da sanin makamar aiki.

Wannan bayani ne a dunkule musamman ga makaranta. Da fari na so a samar da duk list na littattafan da suke a kasa (available) amma aiki ya yiwa mai tattara sunayen yawa. Saboda haka, zamu bayar da dama kowa ya kawo sunan littafin da yake bukata, idan akwai shi a kasa za a gaya masa yadda za a yi ya samu, idan babu shi a kasa za a sanya shi a mala, sai a tuntubi mai littafin a ga yadda za a yi a samar da shi, amma fa sai idan masu bukatar littafin na da yawa.

Marubuta zasuciya tuntubar Kabilu Fagge (Anka) don bayar da bayanai akan littattafan su dake kasa don ya hada mana cikakken list na littattafan.

Haka nan marubutan da suka taba buga littafi, zamu hadu a wani Forum din na marubuta dabam don tattauna yadda kasuwancin zai kasance.

Akwai sauran abubuwa da lokaci bai barmu mun tattauna ba, amma mun sanya a cikin abub

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124