Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M15
Mutun yana da yawan aure-aure saboda bai da wani abin tunawa da shi na jin dadi a zamantakewar aure fiye da ranar angonci. A auren bahaushe babu “honeymoon” kuma yan boko ne kawai suke fita wasanni ko “shopping” da iyalinsu. Zuwa “cinema” ga ma’aurata sabon abu ne da ake ganin tamkar ya saba da addini!

Gaba daya dai a rayuwar bahaushe jin dadi a ranar angwanci da biki kawai ake samunsa. Babu wani abu na musamman da ake bayan angwanci da ya wuce cin abinci tare, idan ma ana yi kenan. Su kam masana halayyar dan adam sun fadi cewa bayan kamar shekara 7 zuwa 8 ma’aurata na shiga wani yanayi da kowa yake jin ya fara gajiya. Abu daya ne yake maganin wannan yanayi, shi ne a dawo da zaman angwanci.

To shi kam bahaushe bai tsara a sake wani biki bayan ya yi aure ba in ba na suna kadai ba. Babu wani abu wai shi “wedding anniversary” a rayuwarmu, sai yanzu da kadan suke yi a Facebook kawai. Tun da dama ba a yi “honeymoon” ba to babu wani abu da ma’aurata za su yi da zai tuno musu da rayuwar angwanci.

A wannan yanayi ne sai kaga bahaushe ya karo aure yana zaton kara aure shi kadai ne zai maganin matsalarsa. Miskinin bai sani ba ita ma amaryar haka zai kara shiga wani yanayin da ita kafin ya karo ta uku. A haka dai zai kare a aure-aure kuma bai ji dadi ba tun da bai gano tushen matsalarsa ba.

A irin wannan rana ta “Valentines” ya kamata ka dauki iyalinka ko da daddare ne don ka yi wani abu mai muhimmanci kamar zuwa “cinema” ko “shopping” da zai dinga tuno maka a rai a lokacin da aka kasa fuskantar juna sai a maimaita. Wannan shi ne amfanin ranar masoya domin a sake bayyana soyayyar da dama tana nan. Kada ka damu da masu ce maka kafirci ne su dama babu jin dadi a rayuwarsu. A haka ma su kansu ba jin dadin rayuwarsu suke ba, don me zaka kwaikwayesu?

______________

*2018

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124