Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M16
Ita mace fara alamar tana jin dadi ne domin idan an sha wahala baki ake yi. Wannan ta sanya duk duniya mai haske take da kima da daraja ko a kasuwar yan mata. Ana siyar da man bleaching amma ba ka taba ganin man yin baki ba. Don haka a dena zagar mana yan matan garinmu don sun shafa “Bio Claire”. Idan ka je Anambra da Enugu ma maza ne suke bleaching.

Idan kai ba ka son mai bleaching to ai ga bakake nan a kasuwa. Amma mun gaji da cin mutuncin da ake yi wa yan matan hausawa don kawai sun shafa man bleaching. Meye ruwanku? Yarinya ta sha kura kuma gidansu ko fanka babu bare AC, ya kake so ta yi bayan samari sun dage sai fara? Yan matan hausawa ku ci gaba da yin duk abin da samari suke so domin ku samu “achievement”. Idan sun dawo aurar bakake sai ku dena bleaching din. Amma duk abin da customer yake so shi mai kanti zai kawo.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124