Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M19
SARKIN KANO DAI...

Cikin abubuwan da BBC ta ruwaito cewa Sarki Muhammmadu Sanusi II ya fada a wani taro da aka yi kwanan nan a Abuja, akwai cewa wai in miji ya saki matarsa to shi ne zai fice ya bar mata gidan. Ya buqaci 'yan majalisa su qirqiri doka ma a kan haka.

Ni kuma sai nake ganin cewa:

Tun a tashin farko, idan mutum ya yi nazarin yadda Mai Martaba ya ajiye maganar, wai mijin ne zai fice ya bar wa matar da ya saka gidan, mutum zai ga cewa, ya riga ya nuna kai tsaye cewa saki laifin namiji ne shi kadai kawai.

Shin haka din ne? A duk lokacin da aka yi saki namiji ne ya zalunci mace? Magidanta da masu tajriba a kan aure su ba da amsa.

Ina batun matar da ta cakume wuyar rigar mijinta ta ce dole sai ya sake ta? Wata ma har da barazanar kisa in bai yi ba?

Ina matsayin matar da mijinta ya kamata da wani a gidansa?

Ina kuma matsayin wacce ta nemi kashe kishiyarta ko dan kishiyar?

Shin Sarki ya kalli wadannan ababe yayin da yake nuna saki laifin namiji ne zalla? Idan ya kalla shin wane hukunci ya yanke wa sakin? Ko kuwa dai ko yaya saki ya zo dole kawai namiji ne mai laifi don haka dole ya bar gidan? In kuma bai kalla ba, to, me ya sa?

Allah bai ce mace ta zauna a gidan miji ba. Amma ya ce ta yi idda don fatan qila auren zai dawo. Kazalika ya nuna a kyautata mu'amala yayin rabuwa a tsakanin matar da mijin, duk dai domin fatan auren ya dawo. Ayoyin Qur'ani duk sun zo da haka.

Wannan shi ne yadda Allah yake lallabar bayinsa wadanda tsawa kadai zai daka mu su su hallake, amma sai ya zabi wannan usulubin na rarrashi da binsu da lalama. Amma shi kuwa Sarkin Kano wanda bai da abin da zai iya cutarwa ko ya yi barazanarsa ga al'umma, shi Sarki ne kawai da bai da aikin da ya wuce a shirya taro a kira shi ya yi ta magana, sai kawai ya zabi ya nuna fusata da yanke wa namiji doka mai tsanani wai dole ya bar gidan matar da ya saka.

To idan ya bar gidan ita matar ce za ta ci da kanta? Ko kuwa in ya bar mata gidan an yi maganinsa ke nan daga saki? Mu qaddara cewa shi namijin ke da laifin sakin, shin qwace gidan daga hannunsa a ba wa matar shi ne ladabtarwa ga sakin? Daga wane kitabur ra'asin aka samu wannan hukunci? Wai ma yaya matar za ta yi da kudin hayar gidan idan gidan na haya ne wanda shi ne akasarin rayuwar da masu sakin suke gidanarwa? Wa zai biya kudin hayar in wa'adi ya qare ga shi kuma an kori miji? Murmushi...

Don Allah Sarki Sanusi ya daina sa baki a harkar aure da iyali, saboda ba batu ne na IMF ko World Bank ba. Duk matsalar da yake tunanin akwaita a harkar iyali, to, Musulunci ya zo da warwararta. Ya duba Qur'ani, ingantattun Hadisai da Fiqhun managartan malamai. Idan ma Sarki yana buqata, zan sa a turo masa littafin حقوق المراة في الاسلام (Right of Women In Islam) na Mujtahidin addini kuma Farfesan Falsafa Murtadha Mutahhari don ya ga yadda ya warware galibin matsalolin nan bisa dogaro da nassi da hukuncin hankali.

Allah ya ja zamanin Mai Martaba.

Ismail Sani Yabo

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124