Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M20
Mai lura da rubutuna zai gane cewa ban fiye bayar da shawara ba. Mafi yawan bayanin da nake na halayyar dan adam ne da kuma yanayin zamantakewa ba wai shawarwari ko wa’azi ba. Gwargwadon yadda ka fahimci yadda halayyar dan adam (psychology) da yanayin zamantakewa (sociology) take kuwa gwargwadon yadda za ka iya tunkarar matsalolin rayuwarka.

Daga baya na gane cewa wa’azin da bai yi dai-dai da halayyar dan adam ko yanayin zamantakewa ba ba zai taba shiga kunnen jama’a don ya yi aiki ba. Don haka shekara dubu malamai suna wa’azin a dena hassada amma su kansu suna yinta. Gasa ita take kawo son kai, shi kuma son kai yake kawo hassada. Gaba daya rayuwar dan Adam kuwa gasa ce tun yana digon “sperm” har ya yi rayuwar dabbobi sannan ya mallaki hankalinsa.

A kowane digon “sperm” akwai miliyoyin kwayoyin halitta. Amma daya daga cikin kwayar “spermatozoa” ce ta kai ga nasarar da aka samar da kai ta hanyar “survival of the fittest”. Tun daga nan son kai yake faruwa. Bayan rayuwa kuma kowane dan Adam ya gano “da arziki a garin wasu gwara a nawa”, har ta kai ga “arzikin a dakinmu”, “a hannuna”, “a bakina”. Duk kuma wanda bai samu ba sai ya ji haushi. Wannan shi ya sanya hassada ta zama tushen dan adam da ba zai taba iya denawa ba. Shi yasa masu wa’azi suke cewa a dena amma su kansu kwararru ne a bangaren.

A imanin kiristoci wannan shi ne zunubin da aka gada daga Annabi Adamu (original sin) da duk kokarinka ba zaka iya rabuwa da shi ba. Suna ganin Allah ya halicci dan Adam da cikakkiyar halitta har sai da Annabi Adamu ta kai yana son yin gasa da Mala’iku sannan shedan ya zugashi ya ci yayan itatuwa. Hatta Qabilu da Habilu gasa da hassada ce ta kai daya ya kashe daya.

A falsafar Musulinci ana ganin zama cikakken mutum shi ne ya fita daga cikin yan uwansa dabbobi. Dukanninmu dabbobi ne sai wanda ya zama “Al’insan”. Gaba daya rayuwar dabbobi kuwa gasa ce, son kai da hassada. Abin da zai janyo mutum ya dena hassadar shi ne ya rabu da abin da al’umma take gasa akansu. Kudi, mata, suna, da nasarorin zahiri na rayuwa. Sai mutum ya hakura da duniya har a cikin zuciyarsa sannan zai iya zama “Al’insanil Kamil”. Amma wannan yana da matukar wuya a al’ummar da ta fi mutunta zahiri fiye da badini.

Akwai matsalolin da mutum zai fuskanta a lokacin da yake son zama “Insanil Kamil”. Da farko dai rabuwa da duniya zai sanya a dinga ganin tamkar asara ya yi a rayuwa domin rashin kayan alatu na nufin talauci a idon mafi yawan mutane. Sannan al’ummar da ba ta gasa za ta rasa ci gaba ne baki dayansa. Domin ci gaba ana aunashi da wani ne ba wai akan kansa ba. Da duk duniya babu wutar lantarki babu wanda zai damu ana dauke wuta. Amma da yake ba a dauke wuta a England sai ya zama ana zagin rashin wuta a Nigeria. Kenan wanda ya ce zai iya rayuwa babu wuta ana yi masa kallon talauci ne da rashin wadata ko da kuwa a zuciyarsa yana jin dadin rayuwa a haka.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124