Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M4
Magana ta gaskiya ka dauki hoton budurwarka ko saurayinki tsirara sannan ka dinga tsoratashi da shi laifi ne a hukumance. Wannan shi ake kira da “revenge pornography”. Mutane su kiyayi irin wadannan laifukan da a addini da doka duka laifuka ne masu tsauri. Wannan babban abu ne da ya fi cutar mata sosai fiye da maza.

Duk abin da aka ce laifin mutum ne tsakaninsa da Allah to a barshi da Allahn. Amma na al’umma to sai a tona al’umma su gani. Don haka nake ganin kuskuren yada bidiyon masu zina amma kuma ba laifi a yada na mai karbar rashawa. Shi wancan tsakaninsa da Allah ne da zai iya yafe masa. Shi kam wannan ya ci amanar al’umma ne da ya kamata al’ummar ta sani.

Kai kuma batun jin dadi don ana tona asirin wasu ba naka ba ne. Idan wani ne yau to fa za ka iya zama gobe. Na ruwa ba ya zagin kada kuma kowa a ruwan nan yake don ba ka san yadda yanayi ko zuciya za ta iya janka ka aikata wani abu ba. Kai dai ba Annabi Yusuf ba ne. Kawai ka dage da addu’ar neman kariyar Allah daga fadawa wani yanayi sannan su kuma wadanda suka fada Allah ya tsare gaba.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124