Tsame Rubutowa
Ismail Sani Yabo
shkr 1 | 1022M7
Mutane suna neman farin ciki a inda ba za su same shi ba. Da yawa ana tunanin katon gida, babbar mota, sabuwar iPhone, yin suna, tara mata, da tarin ilimi su suke kawo farin ciki. A hakikar gaskiya wannan kuskure ne. Hikima ita ce ka gane cewa hakan ba zai sanyaka farin ciki ba. Hakika kuma ita ce ka bari sai ka je gurin sai ka gane babu farin ciki a gurin. Wanda aka bawa hikima kuwa shi ya tara alkhairi mai yawa.

Wadanda suka yi zaton yin kudi ne yake sanya farin ciki sun yi kudin kuma ba su samu farin cikin ba. Wadanda suka dauka auren wani zai basu farin cikin dindindin, sun yi kuma ba su samu ba. Wadanda suka gina katon gida sun gane ba a nan farin cikin yake ba. Duka wadannan hijabai ne da ake zaton farin cikin yana cikinsu amma ba a samu a cikinsu din.

To a ina farin cikin yake? Yana cikin zuciyarka. Idan ka ga dama za ka iya rayuwa ba ka da mota, aure, gida, babbar waya ko kayan sawa masu yawa amma ka fi mai yawo a “private jet” farin ciki. Duk lokacin da ka hakura da wasu abubuwan na duniya za ka gane cewa farin ciki ba a cikinsu yake ba. Wannan shi ne abin da masu zuhudu suka gane suka dena neman duniya. Mutane suna kallon sufaye da shiga mara kyau suna dauka kamar ba su da tunani amma daga karshe na gane sun fi kowa tunani.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124