Tsame Rubutowa
Nana farida Aminu Boukoki
shkr 2 | 1035M1
=====Nana ina Nana===?

To fa ya kamata in anga rakumi a ga Buzu. Na ga Nana Farida to ina Nana Bello? Dn ko na ga bacci ne kawai ke raba ku. Kun shaku sosai. Koda ya ke Basakkata da Bakambama. Farida Aminu kamba. Nana Bello sokoto,masallacin shehu,Gidan da ke kallon gidan abu dan kure. Kunji yadda Nana da Nana suke. Yan shekara daya. Makaranta daya. Aji daya. Katanga ce rabon gidajensu. Sun shaku sosai. Dadi na da su kamun kai. Ga kokarin zuwa makaranta,ko wace iri. Matsala daya da su ke jin ciwo shi ne rashin iya karanta Hausarmu da kyau. Kalli hotonsu: wannan farar yar Sarautar Kamba ce. Wato farida. Dayan kuma yar Sakkwato ce wato Nana Bello, ni na samu wadannan sunayen Basakkata. Farida ko makambama. So na da son labarin annabawa da labarin ibada da sadaukantaka da tarihi. Yanzu haka jiya sai da sunka ce sai na ba su labarin Fillani. Sai na yi recoding a waya sunka saurara.Ga hotonsu:

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124