Tsame Rubutowa
S.I.Z. Jangwarzo
wt 5 | 1060M19
===Ci gaba da darasin 1060M18===

=======Cacici-kacici=======

Kacici-kacici tambayoyi ne ake yi wa mutum a kuma bashi damar ya bayar da amsa.

=====Ire-iren Kacici kacici=====

Kacici kacici ya rabu zuwa iri biyu kamar haka:

A- Mai sauti: Tambayoyin suna zuwa ne a tsarin furta sauti. Misali:

1- Kurkucif kucif = Kwanciyar kare

2- Dillin bari dillin = Kaza bari tono

3- yadda dillin takan yi dillin haka ma dillin takan yi dillin = Yadda kaza takan yi koyi haka ma koyi yakan yi kaza.

B- Mai tambaya:

Tambayoyi ake yi cikin sigar magana. Wannan ya banbanta da mai sauti, domin shi furta tambayar ake yadda kowa zai ji ya kuma gane. A zamanin baya yara ma suna shirya tambayoyi, suna kuma amsawa a junansu. Misalin kacici kacici mai tambaya

1- kulun kulufita = gauta.

2- shirim ba ci ba = baba.

3- baba na daka gemu na waje = hayaki

4- gungume uku gagara dauri = kwai

5- shanu dubu turkensu daya =tsintsiya

6- fura daya dama duniya = farin wata

7- shanu na dubu turkensu daya = tsintsiya d.s

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124