Tsame Rubutowa
S.I.Z. Jangwarzo
wt 8 | 1060M20
==Ci gaba da darasi mai lamba 1060M19==

=======ALMARA=======

Almara na nufin a bayar da labari mai sarkakiya, ko don jin ra'ayin wadanda aka baiwa larin, ko kuma don a yi raha.

======Ire-iren Almara======

Masana sun raba almara zuwa kashi uku kamar haka:

1- Almarar raha.

2- Almarar jin ra'ayi.

3- Almara Mai sarkakiya.

1- Almarar raha: Labari ake bayarwa mai kunshe da saka dariya. Duk wani labari da za a bayar a yi dariya yana karkashin almarar raha.

2- Almarar jin ra'ayi: Ana bayar da labari a kan mutum biyu ko sama da haka akan wani bajinta da suka yi, ko bayar da labarin karya, ko kuma mutum ya fada tsaka mai wuya mafitarsa sai ya rasa wani abun da yake da muhimmanci a wajensa kafin matsalarsa ta warware. Misali:

Watarana sarkin kwadayi ya ce sai ya ci abinci a gidan sarkin rowa. Ya je gidan sarkin rowa, suka gaisa, lokacin cin abinci ya yi. Sarkin rowa ya ga sarkin kwadayi bashi da niyyar tafiya, sai ya zo inda sarkin kwadayi yake zaune ya yi alwala ya sa gabansa gabasa ya ce: na yi niyyar rama salla ta shekara dubu. Da sarkin kwadayi ya ji haka sai shi ma ya ce ba na kishingida a nan kafin a busa kaho. A cikinsu waye yafi daukar abin da ya fi karfinsa.

3- Almara mai sarkakiya: Ana kawo abu mai walar warwarewa, ko lissafi mai kunshe da wahalar amsawa a bukaci mutum ya warware. Misali:

Wata rana tafiya ta samu wani mutum da Akuya da dawa da kuma Kura. Suna cikin tafiya sai suka zo bakin kogi, suka kuma yi rashin sa'a jirgin ruwan abu biyu zai iya dauka a lokaci guda, wato mutum da kuma abu daya, wato Kura, ko Akuya ko kuma dawa. Ya za a yi a haura ruwan.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124