Tsame Rubutowa
S.I.Z. Jangwarzo
wt 6 | 1060M4
2:- Saukakken addini: wasu suna cewa addinin zamani. A cikin saukakkun addini wanda ya fi karbuwa a wajen Bahaushe shine; musulunci. Addinin musulunci ya zo wajen Bahaushe ne ta hanyar kasuwancin da aka yi tsakanin Hausawa da Larabawa. Addinin musulunci shi ne ya kawar da addinin gargajiya, duk da har yanzu akwai sauran maguzawa a Kasar Hausa wadanda babu ruwansu da musulunci. Kiristanci bai samu karbuwa a wajen Bahaushe ba, duk da cewar an fassara littattafan kiristanci da Hausa. Duk Arewacin Najeriya da Kudancin Nijar da Hausa ake amfani a cikin Cocinsu, hakan ya faru ne a dalilin Hausar ce harshen mu'amala a tsakanin kabilun da suke zaune a wannan yankin. Kaso 99.9 cikin dari na Hausawa musulmai ne. Wannan ne yasa Hausawa suka zama musulmai, Bahaushe a yanzu yana kyamar duk wani addini in na na musulunci ba.

"Mishan badda musulmi". Musulunci ne addinin Bahaushe.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124