Tsame Rubutowa
S.I.Z. Jangwarzo
wt 10 | 1060M7
A lokacin da Bahaushe yake yin bauta walau na gargajiya ko na saukakken addini yana tsayar da yin kida da waka. A lokacin da yake yin borin bauta, idan Sarkin bori ya hau, mai kada garaya ko goge ko kidan kwarya za su dagata don sauraron sakon da sarkin bori zai fadawa al'umma. A lokacin da ake bauta irin na musulunci, kama daga sallah da wurudi da sauraron huduba duk ana daina yin kida a wannan lokacin, haka azumi ma, sai bayan an sha ruwa sannan za a yi kida da waka a cikin tashe, ranar sallah ba a yin kida a lokacin sallar idi sai an idar. Wadannan su suka nuna mana lokacin yin bauta ba a yin kida.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124