Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M11
Tabbas sata gidan barawo rance ne,

Bari ka ji labarin wani barawo da matarsa. An ce wai wani barawo ne ya sato tasoshin wasu mutane. Sai ya bai wa matarsa ta kai kasuwa. Da ta je ta sayar, kafin ta dawo gida sai wani barawon ya sace kudin.
Shi kuma gogan naka (barawon watau mijinta) ya matsu ta dawo ta ba shi kudi ya shiga gari sharholiya. Da ya matsu da jira sai ya fito bakin kofar gida. Aka yi katari kuma ya yi bako. Suna cikin magana, sai matar ta zo wacewa cikin gida. Sai ya kasa hakuri ya ce mata:
"Injin an sayar?"
Ta amsa masa da cewa:
"An sayar"
sai ya ce:
"Nawa?"
sai ta ce:
"Yadda ka sayo"
Sai ya noce kai ya ce "Allah Ya mayar da alhairi."

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124