Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M112
==Bakar Al'ada==

Ban gani ba, ballanta in shaida, kuma kada Allah Ya tsayar da ni a ranar shaidu.

An ce wai a Sakkwato, akwai wani wurin wasa wanda samari da 'yan mata ke taruwa da dare. Ba taruwa kawai aka ce ana yi ba, wai har da yarinya za ta tashi tsaye tsakar 'yan kallo, a dinga tayawa har a kai iyakar tsadarta sannan a sallama.

Allah masani, shin idan an taya an bari me zai faru? Wallahi ban sani ba, kuma ban son in sani.

Watakila wannan wani tsohon labari ne wanda ban sani ba ni, amma idan akwai wani mai son tabbabar da wannan labari ko karyata shi yana iya bincikawa.

Tir da wannan al'ada idan har labarinta ya zama gaskiya.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124