Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M114
==Babu Wata MH Sai MH==

Rubutu mai adireshi 1M58 ya yi magana ne a kan samuwar wata Makarantar Hausa a Burkina Faso.

To na tuntubi wanda ya yi rahoto a kanta, watau Abu Hidaya, kuma ya shaida mani cewa, shi kansa yana cikin malaman da suka bai wa malamanta horo. Kenan na yi tambaya ga dan gida.

Abu Hidaya ya ba ni linki, mai dauke da bayanin wannan Makarantar Hausa ta Burkina Faso, sai dai abin da na lura da shi a bayaninsa shi ne, wannan makaranta sunanta KUNGIYAR MAKARANTA, ba Makarantar Hausa ba. Sannan ga abin da na fahinta, shi mai rahoton, shi ne ya ga dacewar ya kira ta haka (Makarantar Hausa), saboda wannan makaranta tana koyar da Hausa ne, kuma a cikin Hausa, kuma don kishin Hausa kawai.

Ba damuwa duk dai yadda abin yake. Wannan Makarantar Hausa ta ainihi ta sanya wa waccan albarka. Allah ya taimake su, ya ba su karfin guiwar ci-gaba a harkokinsu. Kuma MH a shirye take ta taimaka masu da abin da take da shi na nazarin Hausa.

Don samun cikakken bayani a kan wannan makaranta ta Burkina Faso a duba wannan linki da Abu Hidaya ya aiko mani.

juyin-juya-halin-hausawa-burkina-faso.html?m=1

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124