Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M116
==Bakin Da Ya Ci Ya Gode==

Hausawa sun ce bakin da ya ci ya gode, bakin da ya ci bai gode ba, bakin wuta ya fi shi.

A yau din nan, kuma a yanzu din nan, Farfesa A. Muhammad Argungu na Jami'ar Usmanu Danfodiyo, ya bai wa Makarantar Hausa kyautar kwamfuta.

A ganin MH, a ma ganin kowa, wannan ba karamar gudummawa ba ce ga harkokin MH.

MH ta gode a wajenta, kuma ta gode a cikinta, kuma tana rokon duk wanda ya san wannan bawan Allah ya yi masa godiya a madadinta da kuma madadin kowane Bahaushe, saboda taimaka wa MH, daidai yake da taimaka wa Hausa, taimakwa wa Hausa kuwa tabbas taimaka wa kowane Bahaushe ne a duniya.

Allah Ya saka wa Farfesa da alhairi, Allah Ya kara girma da daukaka, sannan Ya yawaita wa Hausa da Hausawa ire-irensa.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124