Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M117
==Amsa-Amo A Waya==

Yau Allah Ya sa kamar yadda masu kwamfuta ke more samun amsa-amo (kafiyya) a cikin sauki, su ma masu waya sun sami nasu.

Duba a sama ka shiga Amsa-Amo.

An sani amsa-amo kan kasance ne a gabar karshe ta dango ko ta baiti, da wannan aiki na MH, za ka iya samun irin wannan amsa-amo.

Kuma akwai amsa-amo mai somawa a farkon dango, da wannan aiki za ka iya samun irin wannan amsa-amo.

Babu wata amsa-amo a tsakiyar dango, sai dai za a iya samun mawakin da ke son yin luguden kalmomi masu sautuka makusunta, a wannan aiki za ka iya samun wannan cikin sauki.

Idan ka shiga wannan sashe na Amsa-Amo da ke sama:

Idan a farko kake son amsa-amo ka zabi FARKO.

Idan a karshe kake son amsa-amo ka zabi KARSHE.

Idan kuma luguden sautuka kake so ka zabi KO'INA

ABIN KULA:
MH za ta bai wa mutum amsa-amo goma a kyauta, sannan idan yana son kari zai biya Naira daya a kan kowace amsa-amo daya.

Da dan abin da za a samu watakila za a iya kara inganta aikin.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124