Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M122
==Abubakar Da Sauran Aiki A Kan Tashe==

Rubutu mai adireshi 1009M26 ya yi mana bayani a kan wani abu game da tashen Zabarmawa, to amma da yake Nijar na da Hausawa, ya kamata mu san wani abu game da yadda suke yin nasu tashe.

Mai wannan rubutu, watau (Abubakar A. Damma), MH na fata zai taimaka ya tambayar mana Hausawan can don jin yadda abin yake. Ga yadda za ka yi tambaya:

1. Nawa ga wata ake somawa?
2. Nawa ga wata ake karewa?
3. Me suka fahinta tsakanin bambancin tashen Zabarmawa da nasu (su Hausawan Nijar).

Kada ka tambayi matasan Hausawa, ka tambayi dattawan Hausawa.

Sannu da kokari Abubakar.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124