Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M129
==Dasuki Ko Dasuqi?==

Wani ya yi tambaya a kan yadda ya kamata a rubuta wannan suna da ke sama.

Abin da zan ce shi ne, babu wata ka'ida ta rubuta wannan suna. Abin da mutum kawai zai yi shi ne ya saurari yadda mutane ke kiran mai sunan. Idan suna amfani da (q) ya yi, idan (k) suke amfani da shi kuma ya yi da shi.

Misali Sarkin Musulmi Dasuqi, an fi amfani da (q) a sunansa. Amma kuma Sambo Dasuki an fi amfani da (k) a sunansa.

To amma idan asalin sunan ake tambaya, to Dasuqi yake ba Dasuki ba.

To amma ka sani, a Hausa da yawa ana juya (q) zuwa (k), a wasu kalmomi da aka aro daga Larabci, kuma wannan suna yana ciki.

Wasu kalmomi masu samun irin wannan canji sun kunshi:

Munafuki ko munafuqi

Hakki ko haqqi

Hakika ko haqiqa

Allah Ya sa mu dace.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124