Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M131
==Ana Kallonku==

Ku sani 'yan Makarantar Hausa ana kallonku, wadanda ke bayan taga, ko masu leke ta katanga suna nan da yawa. Google ya soma bayyanar da ayukanku a shafinsa.

Dole ku canja salo a rubutunku, ku yi rubutu, ku tsaya ku bi rubutun daki-daki, ku gyara duk wata matsala da ke cikinsa. Kada ka yi rubutu, da kammalawa ka aiko, tsaya ka duba, kada ka bar kowane irin kuskure ko da kuwa na aya ne idan ka gan shi.

Kuskure daban, rashin kulawa daban. Kamar yadda mutum bai iya hana kansa kuskure, bai kamata ya bari rashin kulawa ya sa shi kuskure ba.

Ana kallonku!

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124