Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M136
==Ku Lura Da Camfi==

Camfi dai wusu dokoki ne da Hausawa kan aza, masu cewa, kada a yi kaza, ko a yi kaza, ko kaza na sa kaza, ko kaza na hana kaza. Saba wannan doka na kawo mummunan sakamako, a yayin da biyarta ke kawo kyakkawan sakamako, amma a cewarsu.

Duk da yake, camfi ba gaskiya ba ne, amma watakila a karkashinsa mai nazari zai iya gano wata hikima. Misali wani camfi mai cewa "Ba a barin jinjiri shi kadai". Saba wannan doka na sa iskoki su dauke jinjirin, su ajiye nasu. Kowa kuwa ya san renon dan aljani ba karamin aiki ba ne, bayan kuma hasarar nasa jinjirin.

Babu wani aljani da ke daukar dan kowa, amma Hausawa sun aza wannan camfi ne don tabbatar da jirajiransu sun sami kulawar da ta dace. Ga misali, Hausawa na tallabar jinjiri a kan zani ne da suke dunkulawa, idan an bar jinjiri shi kadai, yakan yiyu ya ja zanin ya rufe huskarsa har da hancinsa, inda zai kasa nunfashi. Idan ba nunfashi sai kuwa halaka. Haka Hausawa al'umma ne masu haihuwa da yawa, za ka iya tarar da yara da yawa a cikin gida, barin jinjiri shi kadai babu mamaki wani yaro ya illata shi. Amma ta wannan camfi sai ya sami kulawa.

Hausawa na biyar wannnan doka sau da kafa, ba su barin jirajiransu su kadai gudun aljanu su dauke su, amma a zahirn gaskiya ana neman kariya ne ga su jirajiran daga duk wani hatsari na zahiri da ke iya cutar da su.

Wata mata wadda ta ki biyar wannan camfi wata kika bisa mantuwa, ta bar 'yarta 'yar shekara daya ita kadai a daki a gidan wani biki, bayan awa daya ko da aka zo babbar katifa ta fado wa yarinya, ta hana mata nunfashi, kuma ko da aka zo sai gawa aka tarar. Ta mutu. Haka ya faru a Tashar Kura da ke Sakkwato, kuma ba a fi sati da wannan abu ya faru ba.

Idan kun kula, aljani bai dauke 'yar wannan mata ba. Amma mutuwa ta dauke.

Ku lura da camfi! Idan kun ce karya ne, ti ku duba ko ajwai wata himima da je karkaahinsa.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124