Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M139
==Dauki Dai-Dai....==

An ce dauki dai-dai shi kan kare dawon bagai. Wannan labari da na samu a yau ya faranta mani rai, ba wai don wani zai auri Baturiya ba, a'a, don dai kawai na sami madadin wani labarin wani abu da ya auku a Sakkwato, kuma na rasa gano hakikaninsa.

A yau BBC Hausa ta bayar da labarin wani saurayi, da wata Baturiya ta taso daga kasarsu ta zo don ta aure shi. Wannan ya yi daidai da abin da ya faru a Sakkwato, inda aka ce wata ma ta zo ta yi auren har ta tafi da nata miji.

Ba yin auren, ko rashin yinsa ya dame ni ba, abin da ya dame ne shi ne, irin wannan dauki dai-dai da ake yi wa samarin Hausawa, kuma ni abin bai shafe ni ba, wadanda ya shafa su ne matan Hausawa, don lallai idan ana irin wannan dauki dai-dai, to za su iya rasa mazan aure.

Tun da an ce wata ta zo ta dauka ta tafi, kuma yanzu ga wata nan ta zo za ta dauka, na tabbata sai an koma samun wata ko wasu su ma sun zo sun dauka. Kuma abin bakin cikin (kamar yadda wannan saurayi ya nuna), shi ne matan Hausawa ba su iya soyayya ba. Ba su son mutum tsakanin da Allah. Kuma ya bayar da shawara cewa kowa yana iya gwada sa'arsa a shafukan sada zumunta don ya gani ko zai sami wadda za ta zo ta dauke shi, ko kuma ta aure shi.

Wannan fa tonon silili ne ga matan Hausawa, kuma fa kashin kasuwa ne, duk da yake wasu na iya gaskata zancen wannan saurayi na cewa ba su iya ba, kuma ba su so tsakani da Allah.

Matan Hausawa! Ku gyara idan ku kuka bata. Idan ba haka ba kuwa, to ku sani, dauki dai-dai shi kan kare dawon bagai.

Mai son ya ga wannan labari ya duba a nan:
labarai-51190140

Ga hoton saurayin da Baturiyar daga shafin na sama:

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124