Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M14
=GANDUN HIKIMA 2=

1. Sirrinka kyakkyawa idan ka bayyana,

Tabbas ka san wani gunka zai bidi lashi.

2. Sirrinka mummuna idan ka bayyana,

Ka zam kamar tsuntsun da ba shi da gashi.

3. Mai ba ka shi ne naka in ka san haka,

To yau ka san mai ba ka ka zama nashi.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124