Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M141
==Bari Kuka==

Rubutu mai lamba 1035M2 yana kuka kan Bahaushe ko mambobin wannan makaranta ba su cika yin rubutu ba. Bari kuka, MH ba wurin fira ba ne idan ka tuna, wuri ne na karatu da karantarwa. Don haka ba kowane rubutu za a yi ba a wannan wuri. Wannan yana sa mambobi su yi kaffa-kaffa kan duk abin da za su fada.

Na biyu kuma, wannan wuri bai jima da soma aiki ba, ba kowa ne ya san da shi ba. Idan ka duba ba mu fi kwana hamsin da shida ba a yau da soma aiki. Don haka sai a hankali ne za ka ga kome ya tafi daidai.

Ko ma mene ne, rabu da kowa kama aikinka kawai. Ko na ciki ba su rubuta ba, ai na waje za su karanta. Ci gaba da aiki kawai.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124