Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M145
==Akwai Fatalwa?==

Wani yake tambaya kan wannan magana, ga alama Edita yana cikin aiki, da ya yi mana bayani dalla-dalla. Amma duk da haka zan iya cewa:

Mai nazarin al'ada babu ruwansa da akwai da babu. Shi abin da ya dame shi shi ne, shin masu al'ada sun yarda da samuwar abu? Idan masu al'ada sun yarda da samuwar abu, to akwai abin zai ce. To kenan a nan, dole mai nazarin al'adar Bahaushe ya ce akwai fatalwa, ko da kuwa shi a tunaninsa bai yarda da samuwarta ba, Dole mai nazarin al'adar Bahaushe ya yi maganar MAYE, ko da kuwa bai yarda shi kansa da samuwarsa ba, don Bahauahe a al'adance ya yarda da samuwar maye.

A kan haka, duk wani abu da ya shafi al'ada a gefen akida ko imani, kamar aljani, fatalwa, maita, kandun baka da ire-irensu, ba hurumin mai nazarin al'ada ba ne ya tabbatar da samuwarsu ko akasin haka. Masu kimiya (science) su ne masu bibiyar abu don gano akwai shi ko babu, su ya kamata a tuntuba idan an yarda da hukunce-hukuncensu.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124