Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M146
==Tawa Fahinta Game Da Marubuci==

Wani ya yi magana a kan marubuci kamar yadda masu Education ke kallonsa, wannan rubutu yana da lamba 1009M73 . Sai na ga cewa ni ma ina iya bayyana ma'anar marubuci da manazarci, amma fa a ma'ana ta harshen Hausa ba ta Education ba.

Kamar yadda na fahinta, kowane manazarci marubuci ne, amma ba kowane marubuci yake manazarci ba. A lokacin da mutum ya yi rubutu bayan nazartar abu, a nan a matsayin manazarci yake kuma marubuci. A lokacin da ya kuma yi rubutu bisa radin kansa, a nan kuma marubuci yake kawai ba manazarci ba. Misali duka masu rubuce-rubucen abubuwa na kirkira marubuta ne, amma masu rubuce-rubucen da suka danganci abubuwan da ba na kirkira ba, manazarta ne kuma marubuta. Misali, wanda ya rubuta littafin Magana Jari ce, marubuci ne a wannan lokaci. Sannan wadanda suka rubuta littafin Ikon Allah, a nan gefen kuma manazarta ne kuma marubuta.

Magana Jari Ce, Imam ya rubuta, East ya gyara. Ikon Allah, East da Imam tare suka rubuta.

Idan ka lura, a Magana Jari Ce, suna aiki a matsayin marubuta kawai, a Ikon Allah, kuma suna aiki a matsayin manazarta kuma marubuta.

Wannan tawa fahinta ce kawai.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124