Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M149
==Makadi Da Mawaki==

A harshen Hausa ba wuya a iya bambanta wadannan kalmomi (Makadi da mawaki). Saboda a harshen Hausa, duk wani mai kida da waka, ana iya ce masa mawaki ko makadi. Idan kuma mutum waka kawai yake yi ba tare da ya gwama da kida ba, ana kiransa mawaki kawai.

To amma a nazarin wakar baka ba haka abin yake ba, duk da yake ya yi kusa ga haka. Idan aka ce MAKADI ana nufin mai gwama kida da waka. (Ba a ce masa mawaki). Idan kuma waka kawai yake yi babu kida a ciki, wannan mawaki ne kawai.

Bambanci tsakanin bayanin harshen Hausa da na nazarin wakar baka shi ne wajen mai kida a gwame da waka, ba su kiransa MAWAKI, sai MAKADI ko MAKIDI.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124