Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M155
==Yadda Za A Sa Linki==

Wani rubutu mai lamba 1009M88M1009M182 ya nuna bukatar sanin yadda ake sa linki a rubutu a Magama, to ga yadda ake yi:

Sa linki (link) a Makarantar Hausa mai sauki ne. Sai dai ya kasu gida biyu. Linki na cikin MH, da kuma linki na wajen MH:

1. Linki Na Ciki

Idan ka ga wani rubutu a MH kana son sa linkinsa a rubutunka, a kan kambar rubutun, (kowane abu na da lamba a MH) ka yi kilikin na dama a kwamfuta, ko ka danna wasu layuka guda uku ko makamantan haka, da ke kasan wayarka, sai ka zabi copy link address, ko makamancin haka. Sannan ka tafi inda kake son sawa ka zuba (paste).

2. Linki Na Waje

Idan linkin wani shafi kake son sakawa a rubutunka, kamar na BBC, ka kwafo shi daga address bar din kwamfuta ko na waya ka sa shi a rubutunka.

Idan ka yi dayan wadannan abubuwa shi kenan, Makarantar Hausa za ta yi maka sauran aiki.

Abin Kula

Wannan bayani ya kunshi sa linki a rubutu a Magama, bai kunshi sawa a sashen Shafi ba.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124