Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M159
==Akwai 'Wasu' A Boye==

Wani rubutu mai lamba 1009M95 yana da korafi a kan wani rubutu na MH mai rarrashin 'yan makarantarta su dage don za su iya tafiyar da ita. Rubutun yana da lamba 1M158 to ga amsar MH ga wannan da nata;

To dana, duka lokacin da ga irin wannan rubutu ka dauka akwai (wasu) a cikin baka biyu, wanda ke nufin ba da kai ba.

Zancen hushi da kake magana daga wanda aka taba mahaifinsa, dole zai yi magana. Kamar dai yadda Ali Makaho ke mayar wa Sani Dan'indo martani:

. , ,

To a gaya masa,

duk wanda aka taba babansa,

dole yai magana,

idan dai dan nan dan sunna ne..

(Ali Makaho, wata wakar Sani Dan'ido)

To amma kuma mai Gandun HIkima na cewa

Jan hankali in za ka yo yi a hankali,

Don mai lababe dole ne ya yi sanda.

(Gandun Hikima)

Kai ne da wasu irinka suka fahinci MH, wani ko ya shigo bai san ma me ake yi ba, to irin wannan ai ba abokin fada ba ne. Wanda ya san abin da ake, kuma ka ga ya yi suka, shi kuma dan hasada ne wata kila, ka ga kuma tunda ba a tabbata ba, shi ma bai canacanci fada ba. Tsayawa ake yi a ji korafinsa, idan na da gyara ne sai a karba a gyara, idan kuwa babu wani gyara ai sai a fita batunsa.

Ka daina fada, ka rika lurarsuwa.

Fada, koyaushe ana ajiye shi ne a karshe, a lokacin da babu wani abu da ake iya yi bayanshi.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124