Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M162
==Ma'anar Adabi==

Wata tambaya mai lamba 1063M1 ta nemi bayani kan ma'anar adabi, kuma mun so a ce Edita ya karba wannan tambaya, amma ga alama ayuka sun yi masa yawa. To amma duk da haka, Makarantar Hausa ta dan kokarta ta samo wa mai wannan tambaya amsa daga wani littafi mai suna Fasahar Mazan Jiya ... na Dakta Sadiya Omar (2013). Ga kuma abin da ta ce game da ma'anar adabi:

"Kamusun Hausa (2006) ya kawo ma'anar adabi kamar haka; 'Fannin ilimi wanda ya kunshi labarai da wakokin baka da rubutattu da wasannin kwaikwayo da al'adu da abubuwan fasaha da na hikima.' Shi kuwa Dangambo, (1984) ya bayyana adabi da cewa yana nufin zantuttukan da suka kunshi fasaha ko suke bayyana nau'o'in azanci a fannonin rayuwa iri daban-dabam domin koya wani darasi ga al’umma, watau cikin furuci ko a rubuce.

A takaice za a iya cewa adabi shi ne hoto ko madubin rayuwar al'umma gaba daya wanda zai bayyana fasaharsu da harshensu da al'adunsu. Adabin Hausa ya kasu kashi biyu: akwai adabin gargajiya ko na baka da kuma adabin zamani ko rubutacce. Adabin gargajiya shi ne wanda aka gada daga kaka da kakanni, shi kuwa adabin zamani shi ne rubutacce, wanda ya samu bayan samuwar rubutu a kasar Hausa, shi kuma ya kasu kashi uku: akwai rubutacciyar waka da rubutun zube da kuma rubutaccen wasan kwaikwayo."

Wannan shi ne bayanin da malama ta yi a littafinta. Sai dai mai tambaya ya kula, malamar ba ta bayar da rabe-raben adabin gargajiya ba kamar yadda ta yi wa na zamani. Ta yi haka, ba don rashin sani ba ko mantuwa, a'a, ta yi haka ne don adabin gargajiya bai shafi abin da take rubutu ba a littafinta. Adabin zamani shi ne abin da ya shafi abin da take rubutu a kai, shi ya sa ta farfasa shi don ta kai ga gabar da take son bayani a kai, watau WAKA RUBUTACCIYA.

Idan da bukatar sanin wani abu ana iya sake tambayawa.

Allah Ya amfanar da mu.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124