Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M167
==Duniya Na Da Ban Dariya!==

Wai wani sarki ne ya yi laifi, sai aka kai shi gidan yari. Bayan nan sai aka dauko turmi da tarbaya, aka zuba hatsi aka ce ya yi daka. Bayan ya karbi tabarya sai ya bushe da dariya yana cewa "Duniya na da ban dariya".

Idan wata kila ka musa wannan labari, na tabbata ba za ka musa abin da ya faru ga sarki Sanusi II ba. Bayan tube shi, aka fitar da shi daga garinsa duka a rana daya. Aka kai shi wata jaha duka a rana daya. aka kuma wuce da shi a cikin wani kauye, aka kai shi a tsakiyar dare, inda ba wuta ba ruwa, kuma aka saukar da shi a gidan limamin gari. Wannan ya isa a ce "Duniya na da ban dariya".

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124