Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M17
Sallama,

Makarantar Hausa ta sami labari ba ma daga wuri daya ba, ta ma gani da idonta cewa, wasu masu son shigowa cikinta ba su iya kama ta ta amfani da Opera Mini.

Tabbas haka ne, wata Opera haka take. Wannan kuma (wata kila) yana faruwa ne kasancewar wata Opera na amfani da Google ne don karbar bayanai. Kuma ga shi har yanzu ba mu bai wa Google damar ganin kayan Makarantar Hausa ba. Amma daga yau za mu ba shi izini.

Shawara:

A bi dayan wadannan shawarwari

1. A gwada amfani da wata buroza (Browser) a gani.

2. A dan jira kadan Google ya soma karbar bayanai daga Makarantar Hausa.

Muna bayar da hakuri.


Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124