Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M177
==Mugun Aiki A Cikin Niyya Mai Kyau==

Jihar Kano da Kaduna suna son koyar da yaransu ta hanyar radiyo da talabijin. Wannan koyarwa ta shafi daliban aji shida.

Wannan tabbas niyya ce mai kyau, saboda akwai nuna damuwa da karatun wadannan yara da Corona ta hana su zuwa makaranta.

To amma wannan aiki mugu ne, duk dayake niyarsa mai kyau ce. Dalili, ana sane da cewa Arewa ita ce baya a harkar ilimin boko, wannan ci-baya ana ta zargin juna a kansa, wasu su ce laifin shugabanni ne, wasu su ce laifin malamai ne, wasu su ce laifin dalibai ne, wasu ma cewa suke lafin iyayen dalibai ne.

To duk dai wadda ke da laifi, har yanzu laifin nan na nan.

Idan an kasa tsayawa gaba-da-gaba a koya wa yaro karatu, ta yaya za a iya koya masa shi ta rafiyo?

Ba fa manyan dalibai ba ne. Daliban jami'a su suka cancanci haka in ma haka ake son a yi. Yara ne wadannan, kuma suna gaf da kammalawa, suna bukatar kulawa ta malamai na cikin aji, ba malamai na cikin radiyo ba.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124