Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M178
==Abin Da Wuya: Raba Tallafi Ga Hannu==

Watau akwai matsaloli masu yawa a duniya, kuma kowace matsala za ka ga maganinta na da irin tasa wuya. Amma duk da haka ina ganin kamar maganin matsalar Corona yana kan gaba a kan wuya. Matsala ce da ba a san maganinta ba, ballanta riga-kafi, abin da aka sani, ana iya cewa shi ne mafi inganci shinisantar mutane. Mutum ya nisanci mutane abu ne mai matukar wuya da wahala ko da kuwa ga mutum mawadaci, to ballanta wanda sai ya fita ya samo. Sannan ciyar da gida yana da wuya, ballanta gari, ballanta kasa. Don haka tallafi zai iya yin abin da zai yi, amma ba zai iya hana tagayyarar mutane ba, ballanta ga kasashe masu yawan al'umma. Yaushe aka soma rabawa? Sannan yaushe aka kawo ga mai bukata?

Allah Ya sawwaka!

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124