Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 1 | 1M180
==Tambarin Talaka Cikinsa==

Idan masu kudi, ko Gwamnati na abu, watarana sai dai kawai ka yi shuru. Abin da ya sa na ce haka shi ne, a kwanan baya, wani mai kudi ya tara talakawa ya raba masu kaji da kwai. Sannan kuma na sami labarin cewa Gwamnatin jahar Zamfara ta soma raba wa jama'arta KWAI na kaji.

Tabbas kwai muhuimmi ne wajen gina jiki, kuma idan ba a raba shi da wuri ba, yana iya lalacewa, to amma kwai ba a abincin talaka ba ne, raba wa talaka garin kwaki ya fi muhimmanci, don shi zai iya cika masa cikinsa, kuma ya jima bai ji yunwa ba. Kwai na masu hali ne, su ya kamata su ci shi, amma duk wanda matsayinsa ya kai a ba shi tallafin abinci, kwai bai da wani muhimmanci a gare shi, saboda tsadarsa. Kiret daya na kwai, zai iya sayen kwano uku na garin kwaki, bai wa talaka kwano uku na gari ya fi ba shi kiret daya.

Amma duk da haka an yi kokari Allah Ya saka da alhari. Amma dai a sani, tambarin talaka cikinsa!

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124