Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 7 | 1M197
==Ana Zaman Karya==

An ce wai Bamaguje ne ya shigo birni, ya yi duk abin da yake yi, amma bai ga masussuka ba, abin ya dame shi ya kasa iya boye abin da ke ba shi mamaki game da birni, sai ya tambayi wani da cewa "Shin ina masussuka?" Wanda aka tambaya sai ya karba "Babu!" Bamaguje ya ce "Ana kuwa zaman karya."

Ban dauki wannan magana ta Bamuguje wani abu ba. Amma a yanzu na dauke ta da muhimmanci. Saboda mu da ke birni muna nan muna jiran manoma su yi noma su sussuka su kawo mana mu saye da arha tunda kaka ta yi, amma an ce yanzu a cikin rufeni suke sakawa su boye abinsu, wai su ma sun tsorata da yunwa.

Shi ne na ce tabbas a birni, ANA ZAMAN KARYA.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124