Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
shkr 2 | 1M2
To fa ba wai kayar da giwa ba ne ke da wuya, abin da ke da wuya shi ne birkice ta a fede.

Ma'ana, ba wai kirkirar shafin intanet ke da wuya ba, rayar da shi, shi ne abu mai wuya. Jama'a su ne ke kashe shafi, kuma su ne ke rayar da shi. To kamar haka Makarantar Hausa take. Idan Hausawa sun so rayar da ita za ta rayu. Idan kuma sun so kashe ta sai ta mutu nan take.

Rayar da Makarantar Hausa ya ta'allaka ga samun rubuce-rubuce masu amfani ga jama'a. Da kuma aza hotuna masu kayatarwa. Shigowa a fita ba tare da rubuta kome ba, yana da kyau, amma rubutawa ya fi shi kyau.

Kan haka muke kira ga dukan mambobin wannan makaranta da su daure su rika rubuta wani abu, idan ba su da ta cewa, to su yi tsokaci, idan ba su da abin cewa a tsokaci, to su bayyana ra'ayinsu ta hanyar YABO, SUKA ko Tausayawa.

Da haka wannan makaranta za ta dore, akasin haka kuwa shi zai ga bayanta.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124