Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 10 | 1M202
==Allah Daya Gari Bamban==

Abin yana ba ni mamaki idan aka ce za a a je manyan shugabanni a gaban mutane suna zage-zagen juna su kuma jama'ar kasa suna kallo suna dariya. Wai su a tananinsu wanda ya fi iya bakinsa shi ne ke da alamun nasara a zabe.

Amuruka haka suke yi. idan zabe ya matso, 'yan takarar shugaban kasa kan tsaya dan jarida ya rika tambayarsu su dinga caccar baka, wanda aka kure shikenan yana iya rasa kuri'un wasu jama'a.

A ganina wannan sam ba hikima ba ce. Saboda gaskiya daban, kuma iya magana daban. Duk yadda kake da gaskiya, wanda ya iya magana wani karon yana iya kayar da kai a magana. Amma su Amuruka ga alama ba haka suke ba. Su dai a buga kawai duk wanda ya kasa katmre kansa to shi kenan.

A karawar da aka yi a shekaran jiya Talata tsakanin Trump da Biden, shi shugaba mai ya ci ya sami maki 41, Shi kuma Biden ya sami 48 a cewar wasu. Kenan Biden ga alama ya fi iya magana.

Idan ba ka mutu ba, kome gani kake. idan da rai kuma kana da sauran kallo.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124