Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 6 | 1M206
==Satar Garin Tuwo==

Ban san yadda hukunci yake ba a Kundin Tsarin Mulki, amma na ji ana yada cewa, idan yunwa ta kama mutum ya je wajen mai tuwo ya ce a sa masa abinci mai isarsa, aka ce idan ya kammala ci ya koshi, idan aka tambaye shi kudi ya ce BABU, wai babu abin da za a yi masa. Ban fa sani ba! Ko gaskiya ne ko kuma a'a.

To, idan haka ne ina nufin da gaske ne ba a yi wa mayunwaci hukunci, shin ana yi wa wanda ya saci garin tuwo?

Ban sani ba Wallahi!

Wannan fa wata magana ce da na ji ana cewa wai a Kano sace-sacen garin tuwo wurin nika ya yi yawa, shi ne ya sa wasu masu injuna kirkirar katin shaidar nika. Duk wanda ya kawo nika yana da katin shaidarsa. Wannan dabara ce babba.

Allah Ya yi mana magani.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124