Tsame Rubutowa
Makarantar Hausa
wt 10 | 1M207
==Rassan Hausa==

Wani idan ya ji an ce ana karatun Hausa a makaranta sai ya yi ta mamaki, wai mene ne na karatu?

Da yawa wadanda suka raina karatun Hausa, amma sai sun soma sai su gwammace kida da karatu.

Hausa na da rassa uku, duka dalibin Hausa sai ya bi ta dukansu kafin ya hau reshe daya nata da yake bukatar sarkafewa a kai har a hange shi a kira shi malami. Wadannan rassa su ne:

1. Harshe

2. Adabi

3. Al'ada

A gurguje Harshe na nufin duk wata ka'ida ta magana. Adabi na nufin duk wata fasaha ta magana. Al'ada na nufin duk wata ka'ida ta rayuwa.

A gurguje aka fada, ba a fayyace ba, a kula. Idan ba a gane ba kuma a tambaya.

Don ganin dukan rubuce-rubucen wannan mamba a shiga Makarantar Hausa


Makarantar Hausa, 2021
Waya: 08075946124